(ABNA24.com) A ci gaba da farmakin da suke kai wa kan 'yan ta'adda na nufin tsarkake lardin Idlib, dakarun kasar Siriya sun hallaka akalla 'yan ta'adda 16 yankunan dake gefen lardin na Idlib.
Tashar talabijin Almanar ta ruwaito cewa a ci gaba da kokarin da suke yi na tsarkake kasar daga 'yan ta'adda, dakarun tsaron Siriya sun kai hari kauyen Al-Tamaani'ah dake gefen kudancin Idlib da manyan makaman yaki gami da jiragen sama.
Har ila yau dakarun na Siriya sun yi luguden wuta kan maboyar 'yan ta'addar Annusra dake kauyen Ma'aratu-Nu’uman dake gefen lardin Idlib, inda suka hallaka 'yan ta'adda da dama da kuma jikkata wasu na daban.
A bangare guda, Sojojin Siriya sun sanar da kame makamai masu yawa na 'yan ta'adda a yankunan dake arewacin lardin Hama.
Tsarkake garin Khan Shayhun da Sojojin Siriyan suka yi a kwanakin da suka gabata ya basu damar toshe duk wata hanyar samun dauki da 'yan ta'addar ke samu daga junansu daga lardunan Idlib da Hama.
Wasu yankuna da ke cikin Lardin Hama dake yammaci da lardin Idlib, suna a matsayin larduna biyu da wasu yankunansu suka rage a hannun 'yan ta'addar na Siriya.
/129